AKWAI DARASI CIKIN RAYUWA
Shekaru 10 da suka wuce, Shugaban Kasa Jonathan ya taba bada umarmi wa jami'an tsaro suka toshe wa Kashim Shettima (lokacin yana Gwamnan Borno) hanyar zuwa filin jirgin sama dake Maiduguri har ma sukayi barazanan tumbuke Kashin Shettima daga kujeran Gwamna
Sannan a lokacin ne akayi garkuwa da matan Chibok a Makaranta, ita ma matar Jonathan ta wulakanta Kashin Shettima yana tsaye kusan awa biyu bata masa magana ba lokacin da taje jaje bayan an sace daliban
Amma ku duba kadiyyar da ta faru jiya, tsofin Shugabannin Kasa guda biyu, Obasanjo da Jonathan har da ita matar Jonathan sun tashi tsaye cikin girmamawa suna jiran umarnin Kashin Shattima a matsayinsa na mataimakin Shugaban Kasa ya basu umarnin su zauna
To haka rayuwar take juya tare da bayar da darasi ga masu hankali, mutumin da suka wulakanta jiya yau Allah Ya bashi iko suna jiran umarninsa
Gaskiya mu bi rayuwa sannu a hankali, komai yana da karshensa imbanda ikon Allah, kuma duk wani mulki da karfin iko mai karewa ne imbanda Mulkin Allah Madaukakin Sarki gagara badau din masu badau
Allah Ya sa mu wanye da duniya lafiya
Datti Assalafiy